Sharuddan ijitihadi
Tambaya
Mene ne ijitihadi kuma mene ne sharuddansa?
Amsa
Ana tsinkayar da lafazin ijitihadi ne domin a nuna alamar wani babban bigire mai yalwa na samun wani abu ko yin matukar kokari wurin samun wani abu, don haka anan ana nufin ijitihadi ne da manufar yin kokari wurin karkata zuwa ga abin da ya yi daidai da abin da ke cikin Alkur’ani da Sunnah wurin fitar da hukunce hukunce na shari’a daga cikinsu, da kuma daidaitasu da saukar da su a mahallinsu, domin samun wannan ijitihadin a tsari na asali da aka aminta da shi hakika malamai sun sanya sharudda ga duk wanda yake son haka, sharudda ne masu muhimmanci sosai wadanda za su ba shi damar yin ijitihadinsa bisa ka’idoji sanannu kuma tsararru, daga cikin hakan akwai sanin ayoyin Alkur’ani musamman ayoyin hukunce hukunce da hadisan Annabi tare da sanin hukunce hukuncen da aka share su da wadanda suka sharesu din, hakan sanin fikihu da usulinsa, da kuma sanin hadisi da ilimin da yake rataye da shi na “jurh da ta’adil” wanda da haka ne zai iya bambance ingantaccen hadisi da kuma wanda ba ingantacce ba, da kuma iya sanin hukunce hukuncen da aka yi ittifaki akansu da wadanda aka yi sabani akansu, bai halasta ga mai ijitihadi ya sabawa hukuncin da akayi ijima’i a kansu ba, kuma ya wajaba ga mai ijitihadi ya san abin da lafuzan harshen Larabci suke nufi da kuma salon zancen Larabawa wanda da hakan ne zai san ingancin ma’anar lafazi ba tare da ya rikice masa ba, duk wanda ba shi da masaniya kan ilimin harshen Larabci ba za a iya sakankancewa da iliminsa ba ko ijitihadinsa ba, haka nan an shardantawa mai yin ijitihadi da ya san masadir na shari’a daban daban kamar urfu da kiyasi, sannan ya zama mai iko ne wurin hada dalilai masu tarin yawa a lokacin da aka samu wasu sun ci karo da juna, sannan kuma ya kasance kafin komai ma yana da kwarewa a fannin ijitihadin, inda ma’abota sani za su bayar da shedar kwarewarsa da sauran cibiyoyin ilimi na addini a hukumance wadanda suke da ruwa da tsaki kan manhaji da karantar da shari’a.