Ta’addanci na tunani

Egypt's Dar Al-Ifta

Ta’addanci na tunani

Tambaya

Ta yaya za mu fahimci ayyukan ta’addanci na tunani a wurin kungiyoyin masu kafirta mutane?

Amsa

Shi mutum mai ra’ayin ta’addanci ba ya iya jure tattaunawa domin warware wata matsala da ta shafi ra’ayinsu ko fahimtarsu, daga haka sai su rinka fakewa da hanyar ta’addanci na zancen baka tare da lika zargi na tuhuma ga duk wanda ya yi fito na fito da su, alal misali: da ace  wani mutum zai yi jayayya da wani mai tsattsauran ra’ayi yana mai kokarin gamsar da shi cewa mu’amalar abokanan tarayyar hukuma wadanda ba musulmai ba mai kyau yana daga cikin wajibin abin da shari’a ta tabbatar ta kuma kwadaitar da ayi, sannan kuma ya nuna masa rashin amincewarsa akan yin kalamai na nuna kiyayya ko makamancin haka, to shi mai tsattsauran ra’ayi a irin wannan bigiren yakan yi amfani ne da tunani na ta’addanci a lokacin da ake irin wannan tattaunawar, inda zai ce masa: wadannan mutanen fa kafirai ne, kuma abin da kake kokarin tabbatarwa ya sabawa hukuncin Allah, hakika Allah Ta’ala yace: (Shin ko ba su san cewa duk wanda ya ketare dokar Allah da Manzonsa ba to lallai wutar jahannama ita ce makomarsa kuma zai dawwama a cikinta wannan ya isa tozarci mai girma gare shi) {Tauba 63} sai mai tsattsauran ra’ayi ya rinka kokarin tsorartar da abokin tattaunawarsa da irin wadannan ayoyin.

Yin amfani da wasu alamomi da yawo da hankalin mutane: 

Saboda haka ne babban kalubale na tunanin da yake fuskantar mai tsattusaran ra’ayi yakan kasance mai tsanani ne sosai, tambayoyi akan matukar ayyukansu da makomar abubuwan da suke kira zuwa garesu – so da yawa – su ma ba su da natsuwa akansu, saboda haka mafita akan haka shi ne yin amfani da alamomi da yin wasa da hankalin mutane domin karfafa matsayansu da mafuskantar jama’arsu.

Share this:

Related Fatwas