tsattsauran ra’ayi na tunani

Egypt's Dar Al-Ifta

tsattsauran ra’ayi na tunani

Tambaya

Wani abune mai tsattsauran ra’ayi ke hari wurin yada tunaninsa a tsakanin mutane?

Amsa

Mai tsattsauran ra’ayi na nufar mutane da manufarsa ne domin cika wasu burace-burace masu yawa, musamman:

Motsa kwakwalen mutane- musamman ma matasa- da wasu tunanunnka wadanda ba su yi daidai da tunani na asali wadanda suka dace da tunanin al’umma ba, musamman a wurin ginshikan wayewa mabanbanta da ake bukata.

Sanya kokwanto a cikin tunanunnuka da aikace-aikacen da ke da makoma tabbatacciya, wanda hakan ke haifar da gauraye cikin fahimta a sashen aikata karkatattun ayyuka.

Raunata hadin kan al’umma tare da rarraba kawunansu ta hanyar jefasu cikin kungiyoyi masu banbancin ra’ayi da manufa.

Bata sunan musulunci da musulmai, da kamanta su da munanan siffofi, kawai saboda nuna kaskantar da musulunci da musulmai.

Haifar da yiwa kai ta’addanci ko yiwa wasu mutane na daban, ko kuma yiwa al’umma tare da cutar da su da cuta mafi muni, manufar hakan shi ne tilastawa shugabanni yin abin da suke so wanda ya yi daidai da son zuciyarsu.

Samar da wasu irin mutane masu karamin kwakwalwa da ba su iya banbance gaskiya da karya, ta inda za su yi inkarin tarihi da abubuwan magabata.

Samar da wasu irin mutane da za su kasance suna tozarta rayuwan mutum da ta al’umma.

Kawar da tsakatsaki a cikin lamura, wanda hakan zai haifar da wuce gona da iri da shisshigi tare da nuna ta’assubanci akan hanyar da suke kai.

Canzawa lamura ma’anoninsu, inda suke ganin cewa kunan bakin wake jihadi ne, kuma kashe ran da ba ta da hakki shahada ne.

Share this:

Related Fatwas