Sujuda na tilawa

Egypt's Dar Al-Ifta

Sujuda na tilawa

Tambaya

Mene ne ake karantawa ko yayin da akaji ana karanta ayar da akewa sujada a Kur’ani Mai girma a lokacin da mutum ba ya iya karantawa a cikin lokaci da gaggawa?

Amsa

Ana son musulmi ya karanta wani abu na zikiri da addu’oi matukar dai ba zai iya yin sujada na tilawa ba.

Ita dai sujadar tilawa sunnah ce mai karfi a cikin sallah da wajenta, saboda fadin Manzon Allah sallallaHu AlaiHi wa AliHi Wasallam: (Idan Dan Adam ya karanta ayar da akwai sujada a cikinta kuma ya yi sujadan, shedan yakan koma gefe yana kuka, yana cewa: kaiconsa!) Muslim.

An sanya sharadi na ingancin yin wannan sujada na tilawa ya zama mutum ya na da tsarki na hadasi, da tsarki na jiki da na tufa, da na wuri, tare da fuskantar alkibla da kuma suturta al’aura, sujadar tilawa ba ta inganta sai idan wadannan sharuda sun cika, idan musulmi bai samu daman cika wadannan sharudan ba ko kuma ba ya cikin yanayin da zai iya yin sujadar to ya wadatar masa kawai ya karanta:“Subhanallahi, walhamdulillahi, wala ilaha illallah, wallahu Akbar, wala haula wala kuwwata illa billahil Aliyil Azeem” so hudu, ko wani abu makamancin haka na daga cikin azkaru da addu’oi, wacce akwai yabon Allah Azza wa Jallah a ciki.

Share this:

Related Fatwas