Abin da ake yi a lokacin zare ran m...

Egypt's Dar Al-Ifta

Abin da ake yi a lokacin zare ran mutum

Tambaya

Wani abu ne ya kamata mutum ya yi a lokacin da ya ga wani zai rasu?

Amsa

An sunnata aikata wasu abubuwa ya yin zare ran mutum kamar haka:

Lakkanawa mamaci Kalmar shahada da furtasu a gabansa ba tare da matsawa akan sai ya fada ba, wannan shi ne ma’anar fadin Annabi (SallallaHu AlaiHi wa AliHi Wasallam): (Ku lakkanawa mamatanku La’ilaHa Illallah) Muslim.

Fuskantar da mamaci zuwa ga alkibla, yana mai rigingine a barinsa na dama, matukar hakan ba zai takura masa ba, domin kirdadon kasancewarsa daga cikin ma’abota dama, saboda Al-Barra’u bin Ma’arur – Allah ya yarda da shi – ya yi wasicci da a fuskantar da shi zuwa ga kibla idan ya zo rasuwa, sai  Annabi (SallallaHu AlaiHi wa AliHi Wasallam) ya ce: (ya dace da asali). Baihaki da Al-Hakeem.

Karanta wani abu na Alkur’ani Mai girma, kamar surorin Ikhlas da Yaseen, saboda fadin Annabi (SallallaHu AlaiHi wa AliHi Wasallam): (Ku karanta suratu Yaseen ga mamatanku) Ahmad da Abu Dauda.

Rufe idanuwansa, da rufe labbansa bayan tabbatar da mutuwarsa, domin siffarsa ta cigaba da kasancewa mai kyau, saboda fadin Annabi (SallallaHu AlaiHi wa AliHi Wasallam): (Shi rai idan aka zare shi idanu kan bi shi ne) Muslim. Wannan ya kasance ne a lokacin da ya shiga wurin Abu Salamata – Allah ya yarda da su – a lokacin idanunsa sun bude sai ya rufe su.

  Rufe jikinsa domin gudun kar jikinsa ya yaye, tare da suturta jikinsa da ya cancanza daga idanun mutane, Uwar Muminai Aisha – Allah ya yarda da ita – tace: a lokacin da Annabi (SallallaHu AlaiHi wa AliHi Wasallam) ya rasu (An rufe shi da tufa) Anyi ittifaki akansa, da dai sauran abubuwa makamantan haka na daga cikin sunnoni da malaman fikihu da shugabannin al’umma suka bayyana.

Share this:

Related Fatwas