Abinda ake fada a yayin sujudus-shukur
Tambaya
Mene ne ake fada a yayin sujudus-shukur na godewa Allah, hakanan a yayin sujada na rafkanwa?
Amsa
Idan mutum yayi sujada domin godewa Allah anso masa da ya fadi abinda ake fada a sujudar tilawa, sai ya ambaci abinda yazo cikin hadisin Uwar muminai Aisha Allah ya kara mata yarda daga Annabi SallallaHu AlaiHi wa AliHi wasallam: (Sajada wajhi lillazi khalakahu, wa shakka sam’ahu wa basarahu, bi haulihi wa kuwwatuhi) Abu Daud, Hakeem ya kara da (Fa tabarakallahu Ahsanul khalikeen).
Hakanan anso mutum yace abinda yazo cikin hadisin Ibn Abbas Allah ya kara musu yarda: (Allahummak tub li biha indaka ajra, wa da’a anni biha wizra, waj’alha li indaka zukhra, wa takabbalha minni kama takabbaltaha min Abdika Daud) Tirmizi, hakana anso mutum ya rinka karawa kan wannan addu’ar da yawan yin salati da yawaita yiwa Allah godiya da begensa.