Abin da ake fada a yayin firgici

Egypt's Dar Al-Ifta

Abin da ake fada a yayin firgici

Tambaya

Mene ne ya kamata mutum ya ambata a lokacin da wani abun firgici ya faru kamar girgizan kasa ko makamancin haka? 

Amsa

Yazo cikin sunna mai tsarki cewa idan wani abu ya zo wa mutum da ya firgita shi to ya ce: “ Shi ne Allah Ubangijina wanda bai da abokin tarayya,” saboda abin da yazo daga Sauban Allah ya kara masa yarda daga Annabi S.A.W. ya kasance idan wani abu ya razana shi ya kan ce : “ Huwallahu, Allahu Rabbi la sharika lahu” Nisa’i ne ya ruwaito a cikin sunan Al’kubra.

Wannan hadisin yana nuni ne kan bukatar son ayi addu’a yayin da aka samu abin da ke sanya firgici a zuciyar mutum, ko kuma abin da ke iya firgita shi, daga abubuwa kamar dai wanda yanayi ke haifarwa da wasu abubuwa kamar haka da aka ambata, hakanan malamai sun kwadaitar da yin sallah bayan afkuwar hakan, saboda a cikin yin sallar akwai haifar da natsuwa da kwanciyar hankali, Allah Ta’ala yana cewa : “ Lallai an halicci mutum da yawan butulci, idan abun ki ya same shi sai ya yada kowa yaji, amma idan alheri ya same shi sai ya kame, sai fa masu yin sallah wadanda suke dawwama a yin sallah”{Al’mi’iraj:19-23}.

Share this:

Related Fatwas