Abin da ake aikatawa yayin zare ran...

Egypt's Dar Al-Ifta

Abin da ake aikatawa yayin zare ran mutum.

Tambaya

Me ya kamata mutum ya yi a lokacin da ya riske wanda mutuwarsa ta kusanto?

Amsa

An sunnata kula da abubuwa a lokacin gargaran mutuwar mutum kamar haka  :

1-wanda ya zo gargarar mutuwa akan so a lakkana masa kalmar shahada ta hanyar faurtawa a kusa da shi ba tare da matsa masa kan sai ya ambata ba, wannan shi ne ma’anar fadin Manzon S.A.W. (Ku lakkanawa mamatanku Kalmar La’ilaha illallah) {Muslim ne ya ruwaito).

2-Fuskantar da shi zuwa ga alkibla daga kwance a bangarensa na dama, matukar hakan ba zai takura masa ba, domin fatan kasancewa cikin bangaren dama, saboda Al’barra’a bin Ma’arur Allah ya kara masa yarda, ya bayar da wasiccin a fuskantar da shi ga alkibla idan ajalinsa ya zo, sai Annabi S.A.W. ya ce: (Ya dace da asali…){Baihaki da Al’hakeem ne suka ruwaito}.

3-Karanta wani sashe na Al’kur’ani Mai girma, kamar suratul Ikhlas, da Yeseen, saboda fadin Annabi S.A.W. (Ku karantawa mamatanku suratul Yaseen) {Ahmad da Dauda ne suka ruwaito}.

4-Rufewa mamaci ido, tare da bame labbansa bayan tabbatar da mutuwar mutum, domin ya kasance cikin yanayi mai kyau, saboda fadin Annabi S.A.W. : (Lallai idan aka zare rai ido kan bi inda ran ke tafiya) {Muslim ne ya ruwaito}, wannan ya zo ne bayan da ya shiga wurin Abu Salamata Allah ya kara mu su yarda, bayan rasuwarsa sai idon ya dage sama sai ya rufe masa ido.

5- Lullube mamaci saboda kar ya zama a bude, kuma hakan kan suturta shi, saboda canzawar kamanninsa bayan mutuwa, Uwar muminai Aisha Allah ya kara mata yarda a lokacin da Annabi S.A.W. ya yi wafati ta ce : (An rufe shida lullubi), {Anyi ittifaki a kansa}, tare da aikata wasu abubuwa na sunnoni da malaman fikihu da malaman shari’a suka ambata.

Share this:

Related Fatwas