Amfani da gashin dabbobi a kayayyak...

Egypt's Dar Al-Ifta

Amfani da gashin dabbobi a kayayyakin amfanin yau da kullum.

Tambaya

Mene ne hukuncin shinfidun da ake sana’antawa daga gashin dabbobi.

Amsa

Ya halasta ayi amfani da gashi na asali wanda aka samo shi daga dabbobi, hakanan hukuncin yake akan gashin dabbobi da ire irensu, wanda hakan ya kunshi dukkanin kayayyakin amfani da abubuwan da aka kera daga gashin dabbobin ko abubuwan da suka shafesu, halascin hakan yazo ne cikin fadin Allah Mai girma: (Allah ya sanya gidajenku su kasance wuraren zama gareku sannan ya sanya muku fatun dabbobi na kiragu wuraren zama kamar bukoki  inda kuke amfani da su tare da daukansu cikin sauki  a lokacin tafiye tafiyenku da zaman gidanku hakanan fatun awaki da na rakuma da na jan tumakai su kasance kayan adonku na gida da kuma kayan more rayuwa har zuwa na dan wani lokaci.) [Annahl: 80]

Allah Mai girma ne mafi sani

Share this:

Related Fatwas