Abin da ake ambatawa ya yin firgici...

Egypt's Dar Al-Ifta

Abin da ake ambatawa ya yin firgici

Tambaya

Wani abu ne mutum zai iya ambatawa a lokacin da ya shiga firgici kamar na samuwar girgizan kasa da makamancin haka.

Amsa

Ya zo a cikin Sunnah mai tsarki cewa shi mutum idan ya samu abin da yake firgita shi sai ya ce: “HUWALLAHU RABBI LA SHARIKA LAHU” Saboda abin da ya zo daga Sauban – Allah ya kara masa yarda cewa Manzon Allah (SallallaHu AlaiHi wa AliHi Wasallam) ya kasance idan wani abu ya razana shi yakan ce: “Huwallahu, Allahu Rabbi La Sharika Lahu” Nisa’i. daga Sunan Al-kabir.

Wannan hadisin ya mana nuni ne akan abin da ya kamata mutum ya ambata a duk sanda wani abu ya bashi tsoro ko kuma ya firgita shi, daga cikin abubuwan na bala’ai da sauran abubuwa makamantar haka da aka ambata.

Hakanan malamai sun fifita yin sallah a ya yin faruwar wani abu na bala’I kamar hakan, saboda a cikin sallah akwai natsuwa da kwanciyar hankali, Allah Ta’ala ya ce: (Lallai shi mutum an halicci ne mai butulci* idan sharri ya sameshi sai ya bara* idan kuma alheri ya sameshi sai ya noke* masu kiyaye sallah ne kadai ba sa yin haka sune wanda suke yin sallarsu a koda yaushe). [Al-ma’arij:19-23]

Share this:

Related Fatwas