Gabatar da hankali da akan nakali.

Egypt's Dar Al-Ifta

Gabatar da hankali da akan nakali.

Tambaya

Shin ash’ariyyawa  su na gabatar da hankali ne akan nakali kuma ba sa aiki da Alkitabu wal Sunnah?

Amsa

Wannan zance tsagwaron karya ne daga abokan gaban ash’ariyyawa domin batar da su da kuma bata sunannsu da mazhabinsu,  a zahirin gaskiya su Asha’ira suna aiki ne da hankali wurin fahimtar nakali da nassoshi, su suna riko da hankali ne da nakali tare, saboda wasu nassoshin su na iya rikitarwa ba sa nuna zahirin ma’anarsu, to irin wadannan nassoshin sukan mayar da su ne zuwa ga abin hukuntawa, sai su fawwala ma’anonin nassoshi masu kama da juna zuwa ga Allah Ta’ala, a wasu lokutan sukan bi hanyar tawili wurin fahimtar nassi, inda suke yiwa wasu nassoshin tawili bisa yanda ma’anar harshe yake bayyana da salon zance, alal hakika a bisa wannan tsarin sun gabatarwa Musulunci hidima mai tarin yawa, domin in ba don su ba to an rinka yiwa nassoshi hawan kawara wurin fitar da ma’ana, sai rudadde ya yi zaton ya halasta ayiwa Allah kamanni da sanya masa jiki, - Allah ya tsarkaka daga haka tsarkaka mai girma – misalin hakan shi ne martaninsu ga ayoyin da suke rikitar da mutane kan siffanta Allah Ta’ala da siffofin abin halitta, kamar ayoyin da suke nuna hannu da kwauri zuwa ga ayoyin matattara ma’ana kamar dai fadinsa:(Babu abin da ya yi kama da shi Allah mai ji ne kuma mai gani ne) [Shura:11], sai suka dauki ma’anar ayoyin bisa yanda suke rikitar da fahimta kan kamanta Allah Ta’ala da halittunsa zuwa ga abin da yake abin hukuntawa tabbatuwa ne da dilala, a nan dole za a yi amfani ne da hankali wurin fahimtar nakali da nassi domin riskan ma’anonin da nassi bisa yanda ya dace da matsayin Mahalicci a cikin kwakwale da tsarkake shi SubhanaHu wa Ta’ala.

Share this:

Related Fatwas