Zakkar kudin kamfanoni
Tambaya
Yaya ake fitar da zakkar kamfanonin kasuwanci?
Amsa
Wajibi ne dan kwasuwa ya kididdige hajarsa ta kasuwanci ya yi mata farashi, sannan idan yana da wani karin kudi, ko riba ya hada, sannan ya cire bashin da ake bin kamfani da kuma kudaden gudanarwa, a abin da ya rage ne zai fitar da 2.5% ya bayar da zakka.