Zakkar kudin da aka adana saboda siyan gida
Tambaya
Shin ya halatta a fitar wa kudin da aka adana domin sayen gida da zakka?
Amsa
Idan mutum bas hi da gidan da zai zauna shi da iyalansa, wanda zai haifar masu da kwanciyar hankali da natsuwa, ya kuma zama a fara ajiye kudade a banki da niyya saya wa kansu gidan da za su zauna, to babu zakka akan wadannan kudaden; saboda wannan kudin ana tara shi ne saboda ya biya bukata ta lalura ba ta jin dadi da holewa ba, shi kuma ba a la’akari da ma dukiyar da ake tattala domin samar da bukatu na asali da lalura, idan ana magana akan nisabin zakka, saboda haka babu zakka a ciki, saboda Allah Madaukakin Sarki ya ce: (Suna tambayarka game da abin da za su ciyar, ka ce masu: abin da ya karu akan bukata) [al- Bakra: 219], da maganar Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) cewa: (Babu zakka sai da wadata) [Ahmad].
Amma game da abin da ya yi saura bayan kudin gidan da ake bukata ta lalura game da shi, to wannan akwai zakka akansa idan ya kai nisabi, ya kuma zamana shekara ta kewayo ana ajiye da shi, gwargwadon rubu’in ushari (2.5%) na kudaden.