Amsar kudin inshora daga kamfani
Tambaya
Mene ne hukuncin amsar kudin inshora daga kamfani?
Amsa
Kudaden inshora da kamfunan inshora suke bayarwa abu ne da ya halatta; saboda hakkoki ne da suka samu a karkashin ingatattun yarjejeniyoyin da shari’a ta aminta da su, da kuma nazari mai zurfi da suka nesanta su da kowane irin rudi da shari’a ta hana.