Biyan kudin hidima yanki-yanki.
Tambaya
Shin ya halasta biyan kudin hidimomi kadan- kadan?
Amsa
Biyan kudin aikace-aikace ta hanyar banki yanki-yanki, kamar dai biyan kudin aikin hajji da ummara, ko wanin haka, wanda dai yake da alaka da al’amuran jama’a to ya halasta a shari’ance, matukar kimar kudin da aka bukata a kayyade ne tun farko, sannan anyi yarjejeniya akan cinikin a bayyane tsakanin masu cinikin, kuma akan lokacin da za a biya kudin, irin wadannan cinikayyan suna daukan hukuncin kayan haja ne wurin iya kulla ciniki da za a iya biya nan take ko kuma da kadan kadan, tare da bayar da na kafin alkalami ko aa, tare da Karin farashi wurin biya ya zama kadan –kadan ko kuma ba haka ba.