Biyan kudin Hajji da Umura a yayyan...

Egypt's Dar Al-Ifta

Biyan kudin Hajji da Umura a yayyanke

Tambaya

Mene ne hukuncin biyan kudin Hajji da Umura a yayyanke?

Amsa

Shari’ar Musulunci ta tabbatar da cewa mallakar guzuri da samun abin hawa a aikin Hajji ko Umura sharadi ne na wajibci ba sharadin inganci ba, ma’ana: idan mutum ba shi da su a lokacin aikin Hajji, ba ya nufin cewa Hajjinsa bai inganta ba, hakan yana nufin kawai Hajjin bai wajaba akansa ba, ta yanda idan bai yi aikin Hajjin ba, ba shi da laifi, amma idan har ya dauki haramin aikin Hajji to wajibi ne ya kamala, kuma Hajjinsa ya yi, Hajjin wajibi ya sauka akansa, haka ma mai Umura.

Lura da abin da ya gabata muna cewa: lallai Hajji ko Umuran da aka biyan kudinsu a yayyake sun inganta a shari’ar Musulunci

  

Share this:

Related Fatwas