Yi wa wani Hajji da kudin sadaka

Egypt's Dar Al-Ifta

Yi wa wani Hajji da kudin sadaka

Tambaya

Shin ya halatta a yi wa wani Hajji da kudin sadaka?

Amsa

A asali ana yi wa mamaci aikin Hajji ne daga kudinsa da ya bari, idan ya yi wasici daga a cikin abin da bai wuce kashe daya cikin uku na abin da ya bari ba, ya kuma halatta ya kasance daga cikin kudin wanda zai yi masa Hajjin, ya kuma halatta ya zama daga cikin kudin waninsu; ma’ana: daga dukiyar wani daban, gwargwadon wahala da kudin da aka kashe za a sami lada a wurin Allah Madaukakin Sarki, Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya fada wa A’isha (Allah ya kara yarda da ita) ladan Umurar da ta yi, ya ce: (Gwargwadon wahalarki), ko ya ce: (Kudaden da kika kashe) [al- Bukhari da Muslim].

Saboda haka, shari’a ba ta hana a yi wa wani aikin Hajji da kudin sadaka ba.

Share this:

Related Fatwas