Yi wa mamaci sallah a wurin kabarin...

Egypt's Dar Al-Ifta

Yi wa mamaci sallah a wurin kabarinsa

Tambaya

Shin mamaci yana jin wadanda suka ziyarce shi suka yi masa sallama?

Amsa

Na’am, mamaci yana jin wanda ya ziyarce shi ya yi masa sallama, yana kuma mayar masa da sallamar, daidai da yadda ya dace da tsare- tsaren rayuwar Barzahu, an ruwaito Hadisi daga Buraida (Allah ya kara yarda da shi) ya ce: “Manzon Allah (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) yana karantar da su –sahabbai masu daraja- cewa idan sun tafi makabarta, inda suke cewa: Amincin Allah ya tabbata a gare ku ya ku mazauna wadannan gidaje cikin muminai da Musulmai, mu ma da ikon Allah muna nan tafe, ina roka wa kanmu da kuma samun lafiya da kubuta” [Muslim]. Ibnul Kayyim a cikin littafin “ar- Ruhu” (shafi: 5) yana cewa: “Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya halatta wa al’ummarsa cewa idan sun zo za su yi wa mamata sallama, su yi masu sallama kai tsaye suna Magana da su, sai ya ce: (Amincin Allah ya tabbata a gare ku ya ku mazauna wannan gida na muminai), irin wannan jawabi ana yi wa wanda yake ji, yake kuma da hankali ne, da ba haka ba kuwa da jawabin ya zama mara amfani, domin tamkar ana yi wa abubuwa ne daskararru marasa rai, daukacin magabata na kwarai sun hadu akan haka, an yi ruwayoyi masu yawa da suke nuna cewa lallai mamaci yana sanin ziyarar da masu rai suke yi masa, yana kuma jin dadin haka”. Allah mai girma da daukaka shi ne masani.

Share this:

Related Fatwas