Yiwa marasa lafiya izgilanci.
Tambaya
Ta yaya shari'ar musulunci ta yi gargadi akan tozarta marasa lafiya da yi musu izgilanci?
Amsa
Tozarci da yin izgili ga marasa lafiya ko wani aibi da yake tare da su abu ne wanda shari'a ta hana, kuma mai aikata hakan ya sabawa doka, saboda hakan ya kunshi cutarwa da muzgunawa, bugu da kari wannan halayyar zai iya haifar da matsalar tsaro a cikin al'umma, domin laifi ne, ita kuwa shari'ar musulunci ta zo ne domin ta kwadaitar da mutane rungumar kyawawan dabi'u tare da nesantar cutar da mutane a cikin zantuttuka da ayyuka.
Hukumar bayar da fatawa ta kasar Masar ta na rokon mutane baki dayansu da su yi kokarin datse irin wannan mummunar dabi'a a cikin al'umma, tare da kalubalantar masu aiktawa, da kuma wayar da kan mutane wurin bayyana hadarin da yake cikin irin wannan mummunar aikin, kuma nauyin hakan ya rataya ne a wuyan hukumomin ilimi da masu da'awa da yada labarai, ta hanyar fadakar da mutane illar da yake tattare da aibanta mutane saboda wata lalura da take tare da su, tare da tabbatar da wayar da kan mutane akan yin hanzari a ciki al'umma da kuma kiyaye hakkokin sauran mutane.