Yi wa mamaci sallama a wurin kabari...

Egypt's Dar Al-Ifta

Yi wa mamaci sallama a wurin kabarinsa

Tambaya

Shin mamaci yana jin wanda ya kai masa ziyara ya yi masa sallama?

Amsa

Na’am, mamaci yana jin wanda ya ziyarce shi ya yi masa sallama, yana ma mayar masa da sallamar, yana kuma samun debe kewa da farin ciki da wannan ziyarar, daidai da dokoki da tsare- tsaren rayuwar Barzahu, an ruwaito Hadisi daga Buraida (Allah ya kara yarda da shi) ya ce: (Manzon Allah (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) yana sanar da su –yana nufin sahabbai- cewa idan mun fita zuwa makabarta; inda kowanne daga cikinsu yakan cewa: Amincin Allah ya tabbata ga muminai da musulma wannan gida, in Allah ya yarda muna nan zuwa bayanku, ina rokon Allah ya kiyaye mu mu da ku) [Muslim].

Imam Ibn al- Kayyim a cikin littafinsa “Arruhu: 5” yana cewa: (Lallai Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya shar’anta wa al’ummarsa idan za su yi wa mamata sallama, su yi masu sallama irinta wanda suke magana da shi kai- tsaye, ya ce: Amincin Allah ya tabbata a gareku, muminan wannan gida) wannan salon magana ce da ake yi wa wanda yake ji, yake kuma hankalta, in bah aka ba, maganar za ta zama kaman wanda yake magana da daskararren abu, magabata na gari sun hadu akan haka, akwai Hadisai masu yawa da suke tabbatar da cewa mamaci yana sanin rayayyun da suka ziyarce shi, yana kuma jin dadi da haka).

Allah shi ne masani.

Share this:

Related Fatwas