Izinin Imam, ko shugaban kasa a wur...

Egypt's Dar Al-Ifta

Izinin Imam, ko shugaban kasa a wurin jahadi.

Tambaya

Shin izinin Imam, ko shugaban kasa ba abun shardantawa ba ne a jahadi? Mene ne hatsarin da yake cikin fadin hakan?

Amsa

Izinin Imam ko shugaban kasa sharadi ne daga cikin sharuddan jahadi, wannan na daga cikin abubuwan da ba sa bukatar yawan magana a ciki, Al’kur’ani ya hikaito mana cewa wasu mutane daga banu Isra’ila sun so su yi jahadi sai suka nemi wani abu na farko wanda shi ne samun Imamu “shugaba” wanda za su yi yaki a karkashin jagorancinsa, Allah Madaukakin Sarki ya ce: (Shin ba ka ga wasu mutane daga banu Isra’ila ba ne bayan Musa a lokacin da suka ce wa Annabinsu ka turo mana da jagora mu yi yaki tare da shi saboda daukaka kalmar Allah) [Al-Bakra: 246]. Hakika malamai sun yi ittifaki a tun baya da ma yanzu cewa bayar da umurnin yin jahadi a cikin al’umma ya kasance ne ga Annabi Muhammadu (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) kasancewarsa shugaba ga Musulmai, wanda zai kasance shugaba a bayansa shi ne shugaban Musulmai, ya wajaba akan Musulmai su lizimci al’amarinsa na biyayya a sauran lamura daban- daban, kamar yanda Imamu shi kadai, ko wanda ke wakiltansa ke da hakkin kulla yarjejeniyoyi a karkashin sabon tsari na kasa a zamanance, haka lamarin yake wurin bayar da umurnin yin yaki, da rashin dawowa ga shugaban kasa cikin lamarin yaki, to wuce gona da iri ne cikin hakkinsa, kuma ya cancanci a yi horo a kan hakan, saboda hakan zai iya kai wa ga hatsari mai girma wanda zai iya jefa al’umma cikin abin da ba a zato saboda muninsa.

Share this:

Related Fatwas