Lakanta wa mamaci kalmar shahada da...

Egypt's Dar Al-Ifta

Lakanta wa mamaci kalmar shahada da karanta Alkur’ani a wurin kabari

Tambaya

Shin ya halatta a lakanta wa mamaci kalmar shahada, a kuma karanta Alkur’ani a wurin kabari?

Amsa

Lakanta wa mamaci Kalmar shahada da karanta Alkur’ani a wurin kabari abubuwa ne da ake bukata a wannan lokaci, lallai shari’a ta yi kira da a karanta Alkur’ani mai girma a kowane lokaci; saboda Allah Madaukakin Sarki ya ce: (Ku karanta abin da ya sawwaka a cikinsa) [al- Muzammil: 20], a cikin haka kuma har da karanta wa mamaci Alkur’ani a wurin kabari, kafin da lokacin da ma bayan rufe shi; saboda Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya ce: (Idan wani daga cikinku ya rasu, kada ku dade ba ku yi masa sutura ba, ku yi gaggawar kais hi kabarinsa, a karanta masu suratul fatiha a wajen kansa, a wurin kafafunwansa kuma ku karanta masa karshen suratul Bakra a kabarinsa) [al- Dabaraniy],  da ma Hadisin da Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya ce: (Ku karanta wa mamatanku suratu Yasin) [Ahmad], haka ma lakanta wa mamaci Kalmar shahada a bayan binne shi a mustahabi ne; yana cikin ma’anar Hadisin Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) da ya ce: (Ku lakanta wa mamatanku La’ilaha illalLahu) [Muslim], akwai Hadisai “marfu’ai” da “maukufai” da suka zo akan haka, kuma musulmai sun yi na’am da su a dukan zamunna.

Share this:

Related Fatwas