Aikin mace da tasirinsa a wajen gado
Tambaya
Shin aikin mace zai yi tasiri a cikin hakkinta na gado?
Amsa
Ko ma wane irin yanayi ake ciki sam bai halatta fitan mace zuwa aiki ya sauya hakkinta na ciyarwa akan mijinta ko mahaifinta ba, ko ya dakatar da tabbatattun nassoshi, kuma hakan ba hujja ne na kiraye- kirayen a sauya rabonta a cikin gado ba.
Haka ma la’akari da cewa hakkokin bayi a cikin gado abu ne da ya zama wajibi a bai wa mai hakki daman ya karbi dukan rabonsa, ya kuma zama yana da cikakken hakkin ya yi duk abin da ya ga dama da shi, sawa’un zai amshi abinsa ne da kansa, ko kuwa zai bar wa wani ne, bai halatta a tilasta masa ya bar wa wani ba.