Iddar macen da mijinta ya rasu
Tambaya
Ya adadin iddar macen da mijinta rasu yake a lokacin ta na da ciki?
Amsa
Iddar mace mai ciki ta na zuwa karshe ne da sauke abin da yake cikinta kawai, shin rabuwar saboda rasuwa ne ko saboda wanin haka ne, Allah Mai girma yana cewa: (Mata masu ciki wa’adin iddarsu shine su haifi abin da yake cikin mahaifarsu) [Aldalaq:4] wannan ayar ta kunshi hukuncin macen da mijinta ya rasu ko wanin haka.
Allah Madaukakin Sarki ne mafi sani.