Yi wa mutane izgili

Egypt's Dar Al-Ifta

Yi wa mutane izgili

Tambaya

Mene ne hukuncin wanda yake tsoma bakinsa wurin cin mutumcin mutane kuma yake kutsawa wurin cin zarafinsu?

Amsa

An karbo daga Sa’eed bin Zaid - Allah ya kara masu yarda shi da mahaifinsa – daga Annabi Muhammad (SallallaHu AlaiHi wa AliHi Wasallam) ya ce: (Yana daga cikin mafi girman riba tsawaita baki wurin cin mutumcin musulmi ba tare da hakki ba) Ahmad.

A cikin wannan hadisi akwai tsananta yin gargadi daga Manzon Allah (SallallaHu AlaiHi wa AliHi Wasallam) akan tsoma baki wurin cin mutumcin mutane ko halasta hakan ko kutsawa cikin hakan, ta inda zamu ga ya siffanta hakan da riba, kai ba ma haka ba, “mafi munin riba”to wannan yana hukunta cewa cin mutumcin mutane wani babban laifi ne wurin hukunci, kuma yana daga cikin mafi girman alhaki na zunubi, ba don komai ba sai don bayyana cewa cin zarafin mutane babban laifi ne daga cikin kaba’ir, saboda laifi ne wanda yake rataye da hakkin bayi, don haka ne mai aikata hakan ya cancanci ukuba mai tsanani.

Share this:

Related Fatwas