Zakkar kudi na gado.
Tambaya
Mene ne hukuncin zakkar kudin gado kafin a amsa?
Amsa
Bai wajaba a fitar da zakkar kudin da ka gada ba har sai an karba yazo hannun mai shi tukuna, to daga nan ne za a iya fitar da zakkar wannan kudin, - matukar sharudar fitar da zakka sun cika- wato idan shekara ta zagayo wa kudin daga ranar da aka amsa su ka zo hannu, ko da kuwa shekaru sun shude kudin da yawa, wannan shine hukunci a wurin Malikiyya, kuma ya yi daidai da wata fatawa ta Abu Hanifa.