Budewar diddigen mace a sallah

Egypt's Dar Al-Ifta

Budewar diddigen mace a sallah

Tambaya

Mene ne hukuncin budewar diddigen mace a sallah?

Amsa

Wajibi ne mace ta rufe dukan jikinta –banda fuska da tafuka- a lokacin sallah, wadda kuma take a cikin wani yanayi da idan ta rufe diga- diganta za ta shiga cikin wata damuwa, ko yin haka ya saba da tsarin rayuwa, to tana iya yin koyi da wanda ya halatta budewar diga- digan a cikin malamai masana fikihu, sallarta kuma ta inganta, babu komai.

Share this:

Related Fatwas