Al- kunuti a sallar Asubahi

Egypt's Dar Al-Ifta

Al- kunuti a sallar Asubahi

Tambaya

Mene ne hukuncin lizimtar alkunuti a sallar Asubahi?

Amsa

Lizimtar yin alkunuti a sallar Asubahi shi ne abin da da yawa daga cikin malaman fikihu na da, da na yanzu suka tafi a kai; kuma game da haka ne Hadisi ya zo daga Anas Bn Malik (Allah ya kara yarda da shi) cewa: (Lallai Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya yi alkunuti wata daya yana yin addu’a akansu sannan ya bari, amma game da Asubahi bai daina alkunuti ba har ya bar duniya), wannan Hadisi ne da adadi mai yawa na masana Hadisi suka ruwaito, suka kuma inganta shi, kamar yanda Imam al- Nawawiy da waninsa ya fadi, da wannan ake aiki a mazhabar Shafi’iyya, shi ne kuma mashahuri a Malikiyya, saboda haka mustahabi ne a yi a alkunuti a sallar Asubahi a wurinsu, suka kuma dauki ruwayar share ko dauke alkunuti, da hana yinsa akan cewa wanda aka share ko aka hana shi ne yi wa wasu sanannun mutane addu’a, ba wai shi kansa alkunutin ba.

Duk wanda ya yi alkunuti a sallar Asubahi, to ya yi koyi ne da daya daga cikin malamai masu ijtihadi da ake koyi da su, wadanda aka ba mu umurnin mu yi koyi da su a inda Allah mai girma da daukaka yake cewa: (Ku tambayi masana, idan ku ba ku sani ba) [an- Nahli: 43], dole ne limamai su kula da abin da ya tabba aka kuma saba aiki da shi a masallatai a kasa.

Share this:

Related Fatwas