Hukuncin amsar makwafi
Tambaya
Idan Musulmi ya lalata ko ya batar da wani abu da ba nasa ba, shin dole ne ya biya makwafin abin da ya lalata, ko ya batar, mene ne hukuncin amsar wannan makwafin?
Amsa
Amsar makwafi, shi ne abin da wasu suke kira da “al- Iwadh”, idan masana Kaman bangaren shari’a, ko masu shiga tsakani a rikici su ne suka yi wannan hukuncin, to amfani da makwafin abu ne da ya halatta a shari’a, babu bambanci tsakanin kuskure da ganganci wajen lamuni, haka ma babu bambanci tsakanin mutum ya kasance yaro ne, ko mahaukaci, ko mai barci, ko jahili, duka wadannan abubuwa ba su da tasiri wajen lamuni; inda malaman Fiqihu suka hadu akan halaccin bayar da lamuni, saboda kiyaye hakkoki, da kuma yi wa dukiyoyi zalunci burki, saboda da su ne rayuwa take tafiya. Haka ma sun hadu akan cewa lalata kayan wani, ko bata su dalili ne daga cikin dalilan da suka wajabta bayar da lamuni; idan wani ya lalata dukiyar wani da gangan ko kuskure, dole ne ya bayar da makwafi (lamuni), shi kuma lamunin dukiya ana yinsa ne da kwatankwaci, saboda Allah Madaukakin Sarki ya ce: (Idan za ku rama abin da aka yi maku mara kyau, to ku rama da kwatankwacin abin da aka yi maku) [an- Nahli: 126], da kuma kima a cikin abubuwan da ba su da kwatankwaci, ana kuma kaddara kimar ce da farashin ranar da aka lalata abin, alkali, ko wanda zai kwafe makwafinsa ne suke da hakkin kaddarawa.