Gurbata ruwa
Tambaya
Mene ne hukuncin gurbata ruwan kogi da na tafkuna?
Amsa
Shari’ar Musulunci ta bayar da umurnin kiyaye ruwa saboda shi ne asalin rayuwa; akwai nassoshi masu yawa da suka zo akan haka. Gurbata ruwan kogi da na tafkuna saba wa wannan al’amari ne, da kuma yin watsi da shi, hukuncin Musulunci akan haka shi ne haramci; saboda ta’addancin gurbata ruwa shi ne dai ta’addanci a cikin hakkokin dukan mutane; saboda ya tabbata cewa daukacin mutane suna tarayya akansa, kuma gurbata shi yana kara yawan kudaden da gwamnati take kashewa wajen tsaftace shi, da sake dawo da shi yanda yake saboda a cigaba da amfana.