Dawo da halifancin Musulunci

Egypt's Dar Al-Ifta

Dawo da halifancin Musulunci

Tambaya

Mene ne ma’anar halifanci, yaya halifanci yake a wannan zamanin, shin wai dole ne sai a bi tsarin Kaman yanda masu tsattsauran ra’ayi suke fadi?

Amsa

Halifanci yana nufin: tsayawa a matsayin mai shari’a domin tabbatar da maslahohin addini da na duniya. Halifa kuma shi ne: wanda ya kwafe makwafin wanda ya gabace shi, wasu daga cikin malamai suna ganin cewa ba wani abu ne halifanci ba da ya wuce tsare- tsare na gudanarwa da kundayen tsare- tsaren mulki na zamani suka maye gurbinsu, saboda haka babu bukatar tsarin halifanci da ma’anarsa na da, wannan an yi ne saboda hakan ne ya yi daidai da wancan lokaci, da zamanin, kuma halifanci ba rukuni ne daga cikin rukunnan addini da dole Musulmai su tsayar da shi da surarsa ta da ba, a daidai wannan lokaci kuma wasu suna ganin cewa dole ne a yi aiki wajen dawo da tsarin halifanci da surarsa na da, wasu kuma suna ganin cewa raya tsarin halifanci a wannan zamanin zai tabbata ta hanyar kafa tsarin tarayya “fedaraliyya”; domin hakan zai samar wa da kasashen Musulmai maslahohi masu yawa, tare kuma da cigaban kowane shugaba akan matsayinsa.

Sai dai su kungiyoyin ta’addanci masu tsattsauran ra’ayi sun wajabta wa kawunansu da mabiyansu dawo da halifanci, da nada halifa daga cikinsu, daidai da yanda abin yake a da; abin da ya sanya wasu matasa suka dauki makamai suna yakar gwamnatoci, suna kira wai zuwa ga dawo da tsarin halifanci, suna kuma ganin cewa Hadisan da suka hana a yi fito- na fito da shugabanni ba za su yi aiki tare da wanda ya yi jinkiri wajen samar da tsarin halifanci Kaman yanda shari’a ta bayar da umurni ba, da haka sai suka sauka daga karantarwar shari’a mai girma, suka bi karkataccen gwadabe.

Gaskiyar al’amari it ace: lallai halifanci tsari ne na gudanarwa da na siyasa da ake amfani da shi wajen gudanar da al’amurran addini da na duniya, matukar tsare- tsaren shugabanci na wannan zamanin suna gabatar da wannan aiki a aikace, to babu wani batun tayar da jijiyar wuya da yaki saboda a tsayar da abin da a aikace shi ne yake tsaye, kawai dai ba da surar da kungiyoyin ‘yan ta’adda masu masu tsattsauran ra’ayi suke riyawa ba.

 

Share this:

Related Fatwas