Gargadin Musulunci game da kafirta Musulmi
Tambaya
Ta yaya Musulunci ya yi gargadi game da kafirta Musulmi?
Amsa
Kafirta Musulmi fitina ce mai girma, kuma hatsari ne ga al’ummar Musulmai, wadda yake kekketa hadin kanta, ya kuma raunata karfinta, ya tarwatsa gamayyarta, cutarwar haka yana kai wa zuwa ga rashin daukan jini da dukiyoyi, da hakkoki, da tsaro, gami da amincin al’umma ba a bakin komai ba, lallai addinin Musulunci ya yi gargadi mai tsanani akan fitinar kafirta Musulmai, Allah Madaukakin Sarki ya ce: (Kada ku kuskura ku ce da wanda ya yi maku sallama: ‘kai ba mumini ba ne’, saboda kawai kuna neman tarkacen duniya) [an- Nisa’i: 94], ya kuma sanya wanda yake jifar wani da kafirci ba tare da hakki ba, ya auka cikin hukuncin kafircin, an ruwaito cewa: Manzon Allah (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya ce: (Idan mutum ya ce wa dan uwansa kafiri, to dayansu ya zama). Lallai Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya sanya jifan wani daga cikin Musulmai da kafirci daidai yake da kashe, wannan abu ne da yake nuni zuwa ga hatsarin da yake tattare da haka, inda yake cewa: (Wanda ya tsinewa mumini kaman ya kashe shi ne, haka ma wanda ya kafirta mumini kaman ya kashe shi ne) [al- Bukhari], kuma Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya kara karfafa wannan gargadi nasa game da wannan fitinar, a inda yake cewa: (Mutum ba zai jefi wani da fasikanci, ko ya jefe shi da kafirci ba, face sun dawo kansa, idan wanda ya jefan ba haka yake ba) [al- Bukhari], a takaice dai, duk wanda yake kumajin kafirta Musulmai to ya sani cewa yana kumajin aukawa cikin wuta ne, yana kuma gaggawar shiga cikinta ta mafi gajertar hanya, Allah ya kiyaye mu.