Jahadi a Musulunci kare kai ne ko k...

Egypt's Dar Al-Ifta

Jahadi a Musulunci kare kai ne ko kai hari ne?

Tambaya

Idan muka nufi jahadi da ma’anar yaki, to shin a Musulunci a matsayin kare kai yake, ko kuwa kai hari?

Amsa

Ma’anar jahadi da sunan yaki a Musulunci na nufin kare kai ne ba wai kai hari ba, wanda ya karanta tarihin Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) zai gane haka sosai, domin shar’anta yaki ya yi jinkiri har zuwa bayan yin hijiran Mustapha (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam); domin Musulmai sun cigaba da zama na shekaru masu yawa a garin Makkah suna fuskantar zalunci, da cutarwa, da azabtarwa daga mushirikan Kuraishawa, amma aka umurce su da su yi hakuri da juriya, har dai zuwa lokacin da Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya yi musu umurni – bayan tsanantar muzgunawa – da su yi hijira zuwa Habasha, sannan daga baya Allah ya yi musu umurnin yin yaki, sai Allah Madaukakin Sarki ya saukarwa Annabinsa (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ayar: (An yi umurni ga wadanda ake yakansu lallai an zalunce su, kuma lallai Allah mai cikakken iko ne akan ya ba su nasara) [Al-haaj: 39], duk wanda ya kalli wannan aya mai girma ya samu cewa dalili da manufar yin umurni da yin yaki shi ne kawar da zalunci akan Musulmai, sannan Allah ya farlanta yaki akan Musulmai a inda ya ce: (Ku yaki wadanda suke yakarku saboda daukaka kalmar Allah, amma kar ku yi ta’addanci) [Al-Bakra: 190], manufar wannan ayar a bayyane take domin ta kunshi bayar da umrnin yin yaki saboda daukaka kalmar Allah ne ga wadan yake kai wa Musulmai hare- hare na “Ta’addanci” ba wani abu can daban ba, shin ta’addancin nasu ya kasance domin addinin Musulmai ne ko don wani abu na duniya daban, kamar warwason kayan al’umma.

Share this:

Related Fatwas