Muhimmancin da Musulmai suke bai wa...

Egypt's Dar Al-Ifta

Muhimmancin da Musulmai suke bai wa ilmomin hankali

Tambaya

Shin za a ɗauki muhimmancin da Musulmai suke bai wa ilmomin hankali a matsayin ƙaurace wa Alƙur’ani da Hadisai kaman yanda masu tsattsauran ra’ayi suke faɗi?

Amsa

Muhimmanta ilmomin hankali shi ne muhimmanta Alƙur’ani da Hadisai, saboda da hankali ne ake iya riskar ingancin Alƙur’ani da Hadiasi a matsayinsu na dalilai da hujjojin da ake la’akari da su, sannan a fahimci manufar maganar Allah da Manzonsa ga bayi a cikinsu, hankali ba kishiya ne na nassi ba, a’a kowannensu yana cika ɗan uwansa ne, kaman yanda yake akwai wasu al’amurra da ba zai yiwu a samu cikakken tabbaci akan samuwarsu ta hanyar nassi, ko Alƙur’ani da Hadisai kaɗai, ba tare da hankali ba, irinsu samuwar Allah mai girma da ɗaukaka, haka ma akwai wasu al’amurran da hankali ba shi da daman ya iya riskarsu shi kaɗai, kaman samuwar aljanna da wuta, haƙiƙanin mizani da siraɗi, da ɗabi’ar aljannu da mala’iku. Game da hukunce- hukuncen Fiƙihu kuma irinsu farillan sallah da sunnoninta da ladubbanta, duk da cewa ba hankali ne ya samar da su ba, sai dais hi ne ya iya riskar haka daga nassoshin Alƙur’ani da Hadisai, sai ya riskar da kowanne abu da abin da suka yi kama da juna; saboda haka muhimmanta bai wa hankali wani horo na musamman, da sanin ƙa’idojinsa abu ne mai matuƙar muhimmanci, idan hankali ya lalace, fahimta ma za ta lalace, idan kuma fahimta ta lalace, za mu kauce ga barin manufar da Allah yake nufi da mu, saboda haka ne Allah yake jawo hankulanmu zuwa ga wannan ma’anar a wurare da dama yake cewa: (Lallai a cikin haka akwai ayoyi ga mutanen da suke aiki da hankali) [ar- Ra’ad: 4], da (Lallai mun riga mun bayyana ayoyi ga mutanen da suke fahimta) [al- An’am: 98].

Share this:

Related Fatwas