Muhimmancin da Musulunci ya bai wa ...

Egypt's Dar Al-Ifta

Muhimmancin da Musulunci ya bai wa tsabta

Tambaya

Yaya addinin Musulunci ya bai wa tsafta da tsarki muhimmanci?

Amsa

Addinin Musulunci ya yi kira zuwa ga tsafta da tsarki, inda ya dauke a cikin muhimman abubuwa cikin sakon da ya zo da shi, suka zama wani sashe ne na imani, ya kuma umurci mabiyansa da su kula da su a wurare da dama; saboda tasiri mai girma da suke da su wajen tsarkake zukata, da bai wad an Adam daman daukan nauyi da wahalhalun rayuwa, sai Musulunci ya sanya tsarki ya zama idaba ne mai zaman kansa; kaman alwalla, da wanka, inda ya sanya suka zama sharudda ne na shiga cikin ibadu masu yawa, kaman sallah, da dawafi a dakin Allah mai alfarma, da karatun Alkur’ani, Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya ce: (Ba a karbar sallah ba tare da alwalla ba) [al- Bukhari da Muslim].

A cikin alamun tsafta da tsarki a Musulunci akwai: tsaftar gidaje da wuraren taruwar al'umma, da tsaftace su ga barin bola da dagwalo; saboda maganar da (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya ce: (Lallai Allah mai tsarki ne, yana kuma son abu mai tsarki, mai tsafta ne, yana kuma son tsafta, mai karamci ne yana son karamci, mai baiwa ne yana son baiwa, ku tsaftace –na ga Kaman ya ce- farfajiyar gidajenku, kada ku yi kama da Yahudawa) [al- Tirmiziy].

Share this:

Related Fatwas