Muhummancin ijitihadin cibiyoyi na ...

Egypt's Dar Al-Ifta

Muhummancin ijitihadin cibiyoyi na musamman

Tambaya

Mene ne muhimmancin yin ijtihadin tarayya da kuma cibiyoyi na musamman a rayuwarmu ta yau?

Amsa

Shi ijitihadi na tarayya da na cibiyoyi na musamman na da muhimmanci da manufofi da kima sosai musamman a wannan zamanin namu, domin warware matsaloli na zamantakewa na zamani, saboda lura da wuyan yin ijitihadi na daidaikun mutane tare da irin cigaban da ake samu ko da yaushe mai bibiyan juna a cikin rayuwar yau da kullum gaba dayanta tare da matsalolin da ke tattare da rayuwa, duk da abunda rayuwar ke bukata na zurfin tunani madawwami da kokarin warware lamarin bisa tsari wanda ya yi daidai da zamani, to fa irin wannan mutum daya ba zai iya daukar wannan nauyin ba komai kokarinsa domin kuwa sakamkon fadadar musulunci da karuwar adadin musulmi a kasashen duniya daban daban, saboda haka ya wajaba ijitihadi ya zama aiki ne na mutane da cibiyoyi wanda zai iya dauke nauyin duka saboda shudewar ranaku, haka nan ijitihadi na jama’a yana bayar da damar tattaunawa da yin shawarwari na ilimi ta re da neman taimakon masana kwararru a fannoni daban daban, musamman idan muka yi la’akari da da cewa yanzu muna zamani ne na kwarewa a fannoni, wanda kuma ke zama abu mai wuya matuka ace mutum daya tilo ya kware a fannoni daban daban da sanin wayewa daban daban tare da bunkasa wayewarsa koda yaushe.

Ana lura da cewa ijitihadin mutane da yawa wani nau’i ne daga cikin nau’ukan dacewa da al’umma, kuma hanya ce ta rayuwar bai daya da rangwame na tunani, kuma kofa ne daga cikin manyan kofofin hadin kan al’ummar musulmai.

Share this:

Related Fatwas