Hakkokin masu bukata na musamman.
Tambaya
Shin masu bukata ta musamman sun cancanci a ba su zakkah?
Amsa
Mutumin da ba shi da abin da zai iya biyawa kansa bukatun yau da kullum ko na wadanda suke karkashinsa na daga abinci ko kayan sawa da masauki da jinya da ilmantarwa da sauransu, to duk wanda yake cikin wannan yanayin ya cancanci a bashi zakka, har zuwa lokacin da zai samu dama, abin lura anan shi ne ana kallon yanayin mutum ne ba tare da kallon ya yake ba shin yaro ne ko mai bukata ta musamman ko maraya, idan har mutum ya kasance cikin wadannan da aka ambata to ya cancanci a ba shi zakkah, Allah Ta’ala ya ce: (Ita dai sadaka ana bayar da ita ne ga fakirai da miskinai da wadanda ke aikin tattarawa da kuma wadanda ake son jawo ra’ayinsu da wadanda ake binsu bashi da kuma masu jihadi da matafiya ita zakka dai farilla ce daga Allah kuma Allah Masani ne Mai hikima) [Tauba: 60] don haka mutum zai bayar da zakkah ga wanda ya dace ne kadai, amma idan kuwa bai shiga cikin wadannan ba to ba za a bashi zakkah ba kawai don ya kasance mai bukata ta musamman