Girmama masana fanni

Egypt's Dar Al-Ifta

Girmama masana fanni

Tambaya

Shin ya wajaba a rinka komawa zuwa ga masana kwararru akan wani fanni domin sanin abu da fahimtarsa?

Amsa

Annabi S.A.W. ya koyar damu girmama ma’abota sani kwararru akan fanninsu, duk da irin yawan ilimisa S.A.W. da Allah ya sanar da shi amma ya kasance yana neman shawarar masana kwararru daga cikin sahabbai kan abubuwa da daman gaske na lamuran duniya, wanda hakan yana koya mana komawa ne zuwa ga masana kwararru, Annabi S.A.W. ya kasance ya fayyace sahabbansa masu girma da abin da suka fi kwarewa ko kebanta da shi tare da yaba musu kan hakan, ya kasance yakan ce : (Wanda yafi kowa tausayi cikin al’ummata ga al’ummata shi ne Abuakar, wanda yafi kowa tsananta riko da addininsa shi ne Umar, - Affan ya taba cewa: A cikin al’amarin Allah, shi ne Umar, sannan wanda yafi kowa jin kunya da gaske shi ne Usman, sannan mafi sanin ilimi rabon gado cikinsu shi ne Zaid bin Sabit, wanda ya fisu iya karatun Al’kur’ani Ubayyu bin Ka’ab, mafi sanin halal da haram cikinsu shi ne Mu’azu bin Jabal, ku saurar kuji, a cikin kowace al’umma akwai amintaccenta, to amintaccen wannan al’ummar shi ne Abu Ubaida bin Jarrah) Ahmad ne ya ruwaito.

A cikin wannan hadisin akwai alamu karara da ke fadakar da mutane kan su kasance ma’abota kwarewa a wani fanni na rayuwa wanda zai sa a karkata zuwa garesu a duk lokacin bukata, ko kuma karkata zuwa ga ra’ayinsu a lokacin da aka rasa samun matsaya.

Share this:

Related Fatwas