Siyayya ta hanyar banki
Tambaya
Mene ne hukuncin siyan mota, ko gida ta hanyar banki?
Amsa
Bayar da tallafi na bashi domin siyan gida, ko mota da bankuna suke yi abu ne da ya halatta, babu haramci a cikinsa; sawa’un bankin ya shiga tsakani ne tun a asalin yarjejeniyar tsakanin mai saye da mai sayarwa, ko kuwa kawai bankin ya samar da kudin tallafin bashin ne, wannan ba shi da wata dangantaka da riba.