Kiyaye martaban kasa

Egypt's Dar Al-Ifta

Kiyaye martaban kasa

Tambaya

Mene ce alamomin dake tattare da kira zuwa ga Musulunci domin kiyaye martaban kasa? Kuma mene ne dalilin hakan?

Amsa

Shari’ar Musulunci mai girma ta kira zuwa ga amincin kasashe, yana daga cikin alamomin hakan ne yasa son kasa ya kasance ma’ana ta fidira wacce take fitowa daga jikin dan adam na karkata zuwa ga wannan kasar da take mokamarsa, tare da begensa zuwa ga wurin da ya taso, domin zai kasance ne yana da abubuwan tunawa da wadanda suka rayu tare tun farko na daga masoya da dangi, domin hakan ya bayyana ne cikin aikin Annabi (SallallaHu AlaiHi wa AliHi Wasallam) ya yin da ya nuna son kasa yana daga cikin halayensa.

Daga Anas bin Malik – Allah ya yarda da shi ya ce: (Annabi (SallallaHu AlaiHi wa AliHi Wasallam)   ya kasance idan ya dawo daga tafiya yana hango gidajen Madina sai ya zunkuda taguwarsa domin ta yi sauri, idan kuma wata abar hawa ce sai ya motsa ta) Bukhari.  

Share this:

Related Fatwas