Ziyartar kabarin iyaye
Tambaya
Mene ne hukunci ziyartar kabarin iyaye a duk ranar Juma’a da karanta masu Alkur’ani?
Amsa
Yi wa iyaye biyayya abin so ne a kowane lokaci, bai takaiat da wani yanayi banda sauran yanayi, ko da wani lokaci banda saura ba, ana son a yi a lokacin da suke raye, da bayan sun yi wafati.
A cikin hanyoyin da ake yi wa iyaye biyayya bayan sun koma zuwa ga Allah mai girma da daukaka akwai: ziyartar kabarinsu; saboda gamammiyar maganar Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) da ya ce: (A da na hana ku ziyartar kabarurruka, yanzu ku ziyarce su, domin akwai tunatarwa a ziyartarsu) [Abu Dawud], game kuma da ziyartar iyaye, Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya ce: (Wanda duk ya ziyarci kabarin iyayensa ranar Juma’a, ko kabarin daya daga cikinsu, ya karanta Yasin a wurinsu, ko a wurinsa za a gafarta masa gwargwadon kowace aya ko harafi). Haka ma da karanta masu Alkur’ani, akwai ingantattun Hadisai da suka bayyana haka karara.