Cika alkawarin bakace

Egypt's Dar Al-Ifta

Cika alkawarin bakace

Tambaya

Mace ce tayi bakacen zata yi azumi don Allah a ranakun Litini da Alhamis na tsawon rayuwarta, sai dai mijinta ya hanata saboda yawan rashin lafiyarta, shin ya wajaba sai ta cika alkawarin da ta dauka?

Amsa

Idan mutum bai da ikon cika wani alkawari na bakace da ya yi to kaffara ya wajaba akansa, matukar miji yaki amincewa da matarsa tayi azumi saboda rashin lafiyarta, to nan ya dace matar tabi mijinta, sannan tayi azumin kaffara saboda fadin Annabi S.A.W. : ( Wanda ya yi bakace bai cika ba to sarayar bakacen shi ne ya yi kaffara na rantsuwa) { Sunan Al’kubra).

Share this:

Related Fatwas