Cika alkawari na bakace
Tambaya
Mene ne hukuncin bakace idan wanda ya yi bai iya cikawa ba?
Amsa
Idan mutum yayi wani bakace amma bai samu ikon cika wannan alkawarin ba, ko kuma yayi wani bakace ba tare da ya fayyace ba, to anan ya wajaba a gareshi ya yi kaffarar rantsuwa, saboda fadin Manzon Allah SallallaHu AlaiHi wa AliHi wasallam: (Duk wanda yayi wani bakace amma bai ambaceshi ba to kaffararsa shine kaffarar mai rantsuwa, duk wanda ya yi wani bakace amma ba zai iya aiwatarwa ba to kaffararsa shine na rantsuwa, duk wanda ya yi wani bakace da zai iya cikawa to ya cika shi), kamar dai a misalan da suke zuwa:
Na Farko: Ciyar da miskinai goma ko kuma tufatar da su, wannan yana kasancewa ne bisa daidai gwargwadon ikonsa, sabida fadin Allah Ta’ala cikin bayanin kaffarar rantsuwa: (Kaffararsa shine ciyar da miskinai guda goma na tsakatsakin abinda kuke ciyar da iyalanku, ko kuma tufatar dasu ko kuma ‘yanta baiwa to duk wanda bai samu wannan damar ba to yayi azumin kwanaki uku), hakanan ya halasta ya bayar da kimar kudin abincin ko kimar tufatarwar ga talaka mabukaci.
Na Biyu: Wanda ya gaza wurin yin kaffara ta hanyar ciyarwa ko tufatarwa ko fitar da kimar haka, to yayi azumin kwanaki uku.