Kiyaye rai
Tambaya
Ta yaya Musulunci ya yi kira zuwa ga kiyaye ran dan adam da amincinsa?
Amsa
Musulunci ya yi kira zuwa ga kiyaye dan adam, sai ya sanya kiyaye ran mutum daga cikin manufofin na gaba daya da shari’a tazo da ita domin tabbatar da hakan, ta inda kiyayen ran mutum ya tashi daga matakin hakkoki zuwa matakin wajibai, ita shari’a ba ta tsaya akan kiyaye ran mutum da kare hakkinsa a halin yana raye kawai bane, ai shari’a ne ta wajabta masa daukan mataki ta bin hanyoyin da za su kiyaye rayuwarsa da lafiyar jikinsa inda ta haramta masa cutarwa da munanawa.
Zahirin abin da Musulunci ya yi kira zuwa gareshi kan kare dan adam na da yawa daga ciki akwai: umurni da yin magani da kuma kare kai daga cututtuka, daga ciki akwai hani kan kashe rai ba tare da hakki ba, domin akwai ukuba mai tsanani ga wanda ya aikata hakan, daga ciki akwai hani kan mutum ya cutar da kansa ko waninsa, an karbo daga Abu Sa’eed Al-Khudry – Allah ya kara masa yarda – ya ce:
Annabi Muhammad (SallallaHu AlaiHi wa AliHi Wasallam) ya ce: (Babu cuta babu cutarwa a Musulunci) Al-Hakeem.