Yiwa iyaye biyayya.

Egypt's Dar Al-Ifta

Yiwa iyaye biyayya.

Tambaya

Shin yiwa iyaye biyayya yana kankare zunubai?

Amsa

Hadisai da yawa sunzo a cikin sunnah mai tsarki da suke nuni akan cewa zunubai su na kankaruwa da wasu kyawawan ayyuka, kamar yiwa iyaye biyayya, da kuma hajji karbabbe, da dacewa da daren lailatul kadr,.. daga cikin hadisan da suka zo akan haka akwai fadin Annabi SallallaHu AlaiHi wa AliHi wasallam: (Wanda ya yi hajji bai yi wargi ba kuma bai yi fasikanci ba to zai koma kamar ranar da mahaifiyarsa ta haifeshi ne na rashin zunubi), {anyi ittifaki akansa}. An karbo daga Ibn Umar Allah ya kara musu yarda cewa wani mutum yazo wurin Annabi  SallallaHu AlaiHi wa AliHi wasallam sai yace masa: Ya Manzon Allah ni na aikata wani laifi maigirma, shin akwai hanyar tuna gareni? Sai Manzon Allah yace masa: (shin kana da mahaifiya?) sai yace: a a. Sai Manzon Allah yace masa: (shin kana da inna?) sai yace: Na’am, sai Manzon Allah yace masa: (To kayi mata biyayya). Tirmizi.

Sai dai ya kamata ga mutum kada ya rudu da wadannan ayyukan na falala ya kutsa cikin aikata sabo, kawai saboda dogaro da cewa yiwa iyaye biyayya da sauran kyawawan ayyuka su na kankare zunubai, to fa sai da yin nadama da neman gafara da tuba, ai yin hakan ma shine abu mafi dacewa bayan yin zunuban.

Share this:

Related Fatwas