Sallar biyan bukata.

Egypt's Dar Al-Ifta

Sallar biyan bukata.

Tambaya

Mece ce sallar biyan bukata kuma mene ne hukuncinta da yanda ake yi?

Amsa

Ita sallar biyan bukata wato (salatul Hajah) mustahabba ce, akan yi sallah raka’a biyu ne, sai a karanta fatiha a cikinsu da abin da ya saukaka na Alkur’ani Mai girma, sannan sai a yabi Allah ayi salati ga Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam), sannan sai ayi addu’ar da ta zo a cikin sunnah.

Sallar Hajah ita ce wacce ake yi domin biyan bukata, jumhorin malaman fikihu sun hadu akan cewa yinta mustahabbi ne, akan yi sallah raka’a biyu, inda mai sallar zai karanta fatiha a cikinsu da abin da ya saukaka na Ayoyin Alkur’ani, sannan ya kammala da yiwa Allah Mai girma yabo da yiwa Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) salati, sannan sai ya yi wannan addu’ar da ta zo daga Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) wanda yake cewa: (Duk wanda yake da wata bukata a wurin Allah ko a wurin wani dan adam, to ya yi alwala ya kuma kyautata yin alwalan sannan ya yi sallah raka’a biyu, sannan ya yiwa Allah yabo kuma ya yiwa Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) salati, sannan ya ce: La’ilaha Illalahu Alhalim Alkarim, Subhanallahi Rabbil Arsh Al’azeem, Alhamdulillahi Rabbil Alamin, As’aluka Mujibati Rahmatika Wa Aza’imi Magfiratika Walganimati Min Kulli Birri Wassalamati Min Kulli Ithmi, La Tada’a Li Zanban Illa Gafartah, Wala Hamman Illa Farrajtah, Wala Hajatan Hiya Laka Rida Illa Qadaitaha Ya Arhamar-Rahimin) [Tirmizi da Ibn Majah], wannan shi ne nassin ya yi nuni akan adadin raka’ointa da yanda ake yi, da kuma addu’ar da ake yi a cikinta.

Share this:

Related Fatwas