Sallar neman biyan bukata

Egypt's Dar Al-Ifta

Sallar neman biyan bukata

Tambaya

Mene ne sallar neman biyan bukata, mene ne hukuncin yinta, kuma yaya ake yinta?

Amsa

Mustahabi ne yin sallar neman biyan bukata, ana yin sallah raka’a biyu, a cikinsu ana karanta fatiha da abin da ya saukaka, sannan a yabi Allah a yi masa kirari, sannan a yi wa Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) salati, sannan a yi addu’ar da ta zo a cikin Hadisi.

Sallar neman biyan bukata ana yin ta ne musamman saboda neman biyan bukata, jamhur din malamai sun tafi akan cewa mustahabi ne, sallah ce raka’a biyu, mai sallah zai karanta fatiha a cikinsu, sannan abin da ya saukaka, sannan ya biyo bayan haka da yi wa Allah Madaukakin Sarki yabo da jinjina,, sannan ya yi wa Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) salati, sannan ya yi addu’a ta wannan addu’a da ta zo daga Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam), wanda a ciki yake cewa: (Duk wanda yake da wata bukata a wurin wani dan Adam; to ya yi alwalla, ya kuma kyautata alwallar, sannan ya yi sallah raka’a biyu, sannan ya yabi Allah ya jinjina masa, ya kuma yi wa Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) salati, sannan ya ce: “La’ila illalLahul halimul kareem, SubhanalLahi rabbul Arshil azeem, Alhamdu lilLahi rabbil alameen, As’aluka mujibati Rahmatika, wa aza’imu maghfiratika, wal ganimatu min kulli birrin, wassalamatu min kulli ismin, la tada’a li zamban illa gafartahu, wala hamman illa farrajtahu, wala hajatan hiya laka ridhan illa qadaitaha ya arhamarrahiminina”) [al- Tirmiziy da Ibn Majah], wannan Hadisi ya bayyana adadin raka’o’inta, da yanda ake yinta, da addu’ar da ake karantawa a ciki.

Share this:

Related Fatwas