Ramuwar azumin watan Ramadan
Tambaya
Mene ne hukuncin ramuwar azumin watan Ramadan ga macen da al'ada ya hanata?
Amsa
Wajibi ne mace ta rama azumin da ta sha a watan Ramadan lokacin da al'ada ya zo mata, ba hana ta yi su rarrabe ba; saboda maganar Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) game da ramuwar azumin Ramadan: (In ya so ya yi su a rarrabe, in kuma ya so ya yi su a jere) [Daru Kudniy].