Kiwon kare domin bukata.
Tambaya
Mene ne hukuncin kiwon kare domin wata bukata?
Amsa
Babu laifi a shari’ance ayi kiwon kare domin wata bukata na mutum a rayuwarsa ko a aikinsa, amma da sharadin rashin tsoratar da mutane da karen, ko takura musu da shi, amma dangane da najasar kare da wurin zamansa, to ana daukar fatawar Malikiyya ne da suka ce kare yana da tsarki.