Cinikayya ta hanyar biya kadan- kad...

Egypt's Dar Al-Ifta

Cinikayya ta hanyar biya kadan- kadan

Tambaya

Shin ya halatta a yi Cinikayya ta hanyar biya kadan- kadan, idan hajar ba ta hannun mai sayarwa?

Amsa

Hakinanin wannan mu’amalar ita ce “Cinikayyar murabaha”, wadda Imam al- Shafi’iy ya yi magana akanta a cikin littafinsa “al- Ummu”, yadda take kuwa shi ne:  “Mutum ya nuna wa wani mutum haja, sannan ya ce masa: ka sayi wancan hajar, ni kuma zan b aka ribar kaza a kai”, cinikayyar murabaha da wannan surar abu ne da ya halatta, babu komai a ciki.

Share this:

Related Fatwas